Karfafa dangantaka da sarakuna, magance matsalar tsaro –Batagarawa

Karfafa dangantaka da sarakuna, magance matsalar tsaro –Batagarawa

Bashir Magashi

Tura wannan Sakon

Daga Muawuya Bala Idris, Katsina

Wani malamin jami’a, Dokta Surajo Yakubu Batagarawa, ya yi kira ga jami’an tsaro da su karkafa dangantakar aiki da sarakunan Gargajiya domin samun bayanan sirri wajen magance matsalar tsaro.

Dokta Surajo ya yi kiran ne awajen bikin cika shekaru 30 da kafuwar karamar hukumar Batagarawa da ke jihar Katsina. Ya ce, sarakunan gargajiya, saboda kusancinsu da jama’a, suna da muhimmanci wajen taimaka wa jami’an tsaro sun gudanar da aikinsu.

Dokta Surajo ya ce, jami’an tsaro za su gudanar da ayyukansu cikin sauki ta hanyar tuntuba da yin aiki tare da sarakuna gargajiya. Malamin jami’ar wanda ya gabatar da makala mai taken matsalar tsaro ta kowa da kowa ce, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su taimaka wajen magance matsalar tsaro.

Ya ce, ‘yan Nijeriya suna da rawar da za su taka ta hanyar bayar da bayanai a kan maboyar ‘yanta’adda da masu taimaka masu. Dokta surajo ya ce, dole gwamnati tarayya ta tashi tsaye wajen magance matsalar cin hanci da rashawa, wadanda su ne tushen matsalar tsaro.

Ya yaba wa wadanda suka tsara da gudanar da bikin cika shekaru 30 da kafuwar gundumar Batagarawa, ya ce, taron zai taimaka wajen tattaunawa a kan matsalolin da ke fuskantar gundunar. A lokacin taron, an bayar da takardun yabo ga fitattun mutanen da suka kawo ci gaban Batagarawa ta bangarori daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *