Karimatul Islamiyya tana kara bunkasa -Iyayen Yara

Karimatul Islamiyya tana kara bunkasa -Iyayen Yara
Daga Jabiru Hassan
Makarantar Madarasatul Karimatul Islamiyya da ke layin Mai’unguwa Musa titin Dan Rimi yankin karamar hukumar Fagge tana ci gaba da bai wa yara ilimin addini da na zamani wanda hakan ya sa iyaye da masu rike da yara suke godiya ga makarantar.
Wakilinmu wanda ya ziyarci makarantar ya ruwaito cewa iyayen yara sun nuna gamsuwarsu bisa yadda makarantar take bayar da ilimi ingantacce kuma tun daga tushe wanda hakan ke nunar da cewa daliban makarantar za su ci gaba da kasancewa abin misali duba da yadda suke samun kulawa ta musamman.
Bugu da kari, madarasatul Karimatul Islamiyya layin Mai’unguwa Musa ta yi fice wajen bayar da tarbiyya da koyar da karatu ga dalibai cikin yanayi mai kyau duba da yadda kowa yake kokarin kai dansa wannan makaranta domin samun ilimi ingantacce da kuma bayar da tarbiyya mai kyau kamar yadda ake gani a yau.
Shugabar makarantar, Malama Binta Idris ta sanar da cewa an kafa makarantar ne a shekara ta 2011 da dalibai 7 da kuma malamai guda 2, amma a cewarta, yanzu makarantar tana da dalibai 1,700 da kuma malamai 17.
Malama Binta ta kuma jaddada cewa za su ci gaba da bayar da ilimi ga dalibai maza da mata ba tare da nuna gajiyawa ba musamman ganin yadda al’umma suke yaba wa tsarinsu na bayar da ilimi.
Haka kuma Malama Binta Idris ta gode wa iyaye da malamai da kuma masu tallafa wa makarantar wanda hakan ya sanya ake aikin bayar da ilimi da koyar da tarbiyya ga yara kanana masu tasowa, inda ta yi kira ga mutanen da Allah ya bai wa iko da su taimaka a sami karin ajujuwa a makarantar da yin rumfa a gaban ajujuwan da ake da su, domin ganin ana ci gaba da rage cunkoso a makarantar.
Daga karshe Malama Binta ta jinjina wa gwamnatin jihar Kano saboda kokarin da take yi wajen kyautata yanayin koyo da koyarwa a makarantun jihar Kano, tare da shawartar iyayen yara da su kara bai wa yaransu kwarin gwiwar yin karatu tun daga tushe.