Karin farashi, barazana ga harkokin kasuwanci -In ji shugaban Hamir inbesment

Karin farashi, barazana ga harkokin kasuwanci
Daga Wakilinmu
Yawan karin farashin kaya da kamfanoni musamman na masarufi na matukar barazana da kuma kawo cikas ga harkokin kasuwancin jihar Kano da kasa baki daya ya zama wajibi gwamnati ta shigo domin takawa kamfanonin burki, ko masu karamin karfi za su samu sauki.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Alhaji Hamisu Rabi’u Jingau, da ke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar kwanar Singa Kano.
Da yake tsokaci a kan cika shekaru ashirin da a kan dimukuradiyyar kasar nan kuwa, Alhaji Hamisu Rabi’u Jingau ya ce, an samu ci gaba musamman yadda har yanzu kasar nan ke dunkule a matsayin kasa daya ba tare da ta wargaje ba, duk da fuskantar matsalolin da kasar take fuskanta musamman a kan tsaro.
Saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta kara kokarin da take yi a kan tsaro, shugaban kamfanin na HAMIR INBESMENT ya jawo hankulan shugabanni su rika kwatanta gaskiya da tsoron Allah a gurin tafiyar da mulkinsu.
Ya yi amfani da wannan dama da kira ga al’umma da su taimaka wa gwamnati a kan tsaro sannan malamai, sarakuna da sauran masu fada aji da a zauna domin kawo karshen matalolin da ke addabar kasar nan, musamman na tsaro.
Daga karshe, ya ce, tsarin mulkin kasar nan da ake kokarin canzawa ko kuma gyara ba za’a samu canji ba har sai al’umma sun canza daga halaye marasa kyau zuwa ga halaye na gari.