Karrama Sarkin Gombe, karrama jihar Gombe -MD Galaxy

Tura wannan Sakon

Danjuma Labiru Bolari, Daga Gombe

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III da lambar girmamawa ta kasa ta CFR.

Wannan karamci ba Sarkin Gombe kawai aka yi wa ba, al’ummar jihar ne baki daya aka karrama, a cewar manajin daraktan na kamfanin Galady Backbone, Farfesa Muhammad Bello Abubakar.

Farfesa Muhammad Bello, ya bayyana hakan a lokacin da yake taya Sarkin na Gombe murnar samun lambar karramawar ta kasa, inda ya ce, iya salon mulki da taimakon al’umma ne ya jawo wa Sarkin wannan karramawar.

Ya bayyana hakan ta cikin wata takardar bayani mai dauke da sanya hannun mai taimaka masa ta bangaren yada labarai, Tasiu Muhammad Pantami, da ya aike wa wakilinmu.

Farfesan ya ce, Sarkin ya jima da cancantar irin wannan lambar karramawa ta kasa ta CFR, inda ya ce, wannan somin tabi ne, ya ce, yana da yakinin Sarkin zai iya samun lambar karramawa ta kololuwa a Nahiyar Afirka, ko ma a kasashen daular Larabawa nan gaba.

Farfesa Abubakar, ya kuma jinjina wa shugaban Nijeriya Muhammad Buhari, bisa ganin cancantar Sarkin na Gombe da wannan lamba mai girma ta CFR.

Daga nan sai ya yi addu’ar fatar alkhairi da gamawa lafiya ga Mai Ambaliya: Kungiyar ‘yan Gwari ta jajanta wa mutanen Kano, Jigawa Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, sannan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa Sarkin hadin kai da goyon baya, kana su kara taya shi da addu’a domin gamawa lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *