Karyewar darajar Naira, karyewar ‘yankasuwa -Sani Ahmad

Karyewar darajar Naira, karyewar ‘yankasuwa -Sani Ahmad

Karyewar darajar Naira, karyewar ‘yankasuwa

Tura wannan Sakon

Daga Hussini Kano

Sakamakon ci gaba da karyewar darajar Naira ya sa yawancin ‘yan-kasuwa musamman kanana sun shiga cikin zulumi wanda ya kamata gwamnati ta gaggauta daukar mataki a kai ko ‘yankasuwa sa samu sa’ida, idan kuma ba haka ba kasuwancin su zai iya durkushewa.

Bayanin haka ya fito daga bakin wani dan kasuwa da ke sana’ar sayar da maganin Dabbobi da ke kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi a Kano, Alhaji Sani Ahmad, a lokacin da yake nuna damuwarsa a kan yadda farashin Naira ke ci gaba da durkushewa ita kuma farashin Dala ke kara hauhawa a kasuwannin Duniya.

Alhaji Sani Ahmad ya bayar da misali da idan dan kasuwa yana shigowa da kwantaina na kaya guda 10 daga waje yanzu yana da wahalar gaske ya iya shigo da guda 6, sannan wadansu kayan dole sai an shigo da su daga wadansu kasashen.

Ya ce, wani abu kuma da yake addabar ‘yan-kasuwar jihar Kano, shi ne matsalar tsaro domin har yanzu akwai wadansu bakin ‘yan-kasuwar da ba ya iya shigowa jihar domin gudanar da harkokin kasuwanci wannan matsala ta rashin tsaro ya kawo nakasu sosai a kan harkokin kasuwancin jihar da na kasa baki daya.

Matashin dan-kasuwar s ya yi amfani da wannan dama da shawartar gwamnatin jihar Kano cewa, duk lokacin da za ta nada mukami a kan ‘yan-kasuwa ta tabbatar ta zabo daga cikin ‘yan-kasuwa wadanda suka san matsalolin kasuwanci da ‘yan-kasuwa.

Ya kuma nuna farin cikin sa a kan yadda ake kara samun ci gaban harkokin kasuwancin sayar da maganin Dabbobi a jihar Kano wannan nasara ce wanda a shekarun baya abin ba haka yake ba.

Daga karshe ya ya yi kira ga ‘yan kungiyar da ke jihar Kano da su ci gaba da yin biyayya ga shugabancin kungiyar, sannan su tsare gaskiya da amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *