Kashe Deborah ba daukar doka a hannu ba-Sherif Auwal Siddi

Deborah
Danjuma Labiru Bolari Daga Gombe
Alhaji Auwalu Saddik Bolari, daya daga cikin tsofaffin mawakan yabon Manzon Allah, a Gombe, yanzu haka shi ne shugaban kungiyar Ushakun Nabiyi ta kasa, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wadansu malamai suke ganin kashe Deborah wadda ta yi batanci ga Manzon Allah da cewa, daukar doka ne a hannu.
Auwalu Saddik, ya nuna fushinsa a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce, wadansu mabiya addinin Kirista sun raina Musulunci, wanda hakan ta sa ake ci gaba da samun masu aikata batancin ga Annabi.
Ya ce, kamata ya yi duk wani ko wata da ya yi ko ta yi batanci ga Manzon-tsira, a kashe shi domin babu wani a duniya da ya fi Annabin daraja. Sherif Auwal Bolari, ya kara da cewa, marasa kishin addinin Musulunci da ba sa son duniya ta ga laifinsu suke cewa, a hukunta wadanda suka kashe Deborah.
“Ba Deborah kadai ba duk wanda ya yi batanci ga Manzo ya zama dole a kashe shi, domin ya zama izina ga mutane irinsa, in ji shi. A cewarsa, duk bayanan da malamai suke yi da fatawa da suke bayarwa a kan abin da Deborah ta yi wadansu na ganin kamar an wuce gona da iri ne, inda ya ce, tabbas ba haka ba ne, ya ce, duk wanda ya taba Annabi jininsa ya halatta. Sherif Auwal Siddi, ya kara da cewa, su sha’iran Manzo ko a cikin waken da suke yi suna fadakar da mutane irin darajojin da Annabi yake da su kuma shi badadin Allah ne.
Ya yi amfani da damar wajen jan hankalin shugabannin addinin Kirista da cewa, su fadakar da mabiyansu cewa, su daina taba darajar addinin Allah wanda hakan zai ci gaba da kawo tashe-tashen hankula da rasa rayuka. Ya ce, ba a taba jin wani musulmi ya yi batanci ga wani Kirista ko cin zarafin littafin Injila ba amma Kiristoci ba cin zarafi da batancin da ba sa yi wa addinin Musulunci da littafin Allah.
Daga nan Auwal Bolari, ya yi kira ga hukumomi da suka tsare wadanda suka kashe Deborah da su gaggauta sako su saboda ko a wajen Allah ba su yi laifi ba, kuma ci gabada tsare su zai sa fushin Allah ya sauka a kansu.