Kashe-kashe a Arewa: Sarkin Musulmi ya yi horo da alkunutu

, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III

, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III

Tura wannan Sakon

Daga Saminu Abdullahi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buqaci al’ummar Musulmi su fara gudanar da addu’o’i na alqunutu game da kashe-kashen da yankin arewacin Nijeriya.

Kazalika sarkin ya hori dukkan masallatai da majalisun tattaunawa a fadin Nijeriya da su dage da addu’o’i a irin wannan lokaci na bala’o’i domin neman tausayin Allah.

Wata sanarwa daga qungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) wadda sarkin Musulmi ke jagoranta ta ce, an yi kiran ne saboda ya zama dole.

“Kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaqanta su gaba-gadi kamar yadda muka gani a Sakkwato da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga a jihar Borno” in ji shi. A cikin sanarwar da babban sakataren JNI, Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu, sarkin Musulmin ya koka matuqa.

A farkon makon da ya gabata,‘yan fashin daji sun qona mutune 23 da ransu a cikin motar fasinja a jihar Sakkwato, sannan suka sake kashe uku tare da sace wadansu da dama; ‘yan bindiga sun kashe mutum aqalla 15 a masallaci a jihar Neja; an kashe kwamashina a jihar Katsina a cikin gidansa.

Sanarwar ta ce, sarkin Musulmi ya shawarci dukkan majalisun ilimi da na tattaunawa da makarantun allo da kuma dukkan shugabannin qungiyoyin Musulmi da su duqufa wajen yin addu’o’in.

Ta qara da cewa, an buqaci mutane su dinga yin addu’o’in ne ta hanyar abin da sanarwar ta kira “Qunootun-Nawazil, wadda ake yi a lokutan bala’i”.

Saboda haka ana kiran Musulmi da su duqufa wajen yin alqunutu a raka’ar qarshe ta dukkan sallolin farilla da na nafila domin neman taimakon Allah. Haka nan sanarwar ta alaqanta tabarbarewar lamura da ayyukan ‘yan Nijeriya, tana mai cewa, cin hanci da kuma dabar siyasa sun zama abin tinqaho. A qarshe, ta yi kira ga gwamnatoci da su miqe tsaye wajen aiwatar da

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *