Kashe-kashen shanu: Abia za ta biya Fulani diyya

gwamna Okezie Bictor Ikpeazu
Gwamnatin jihar Abiya ta fara biyan diyya ga mutanen da hari da aka kai a sabuwar kasuwar shanu ya shafa.
Bayanin na zuwa ne bayan da gwamna Dokta Okezie Bictor Ikpeazu na jihar ya gana da al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar kan harin. Sarkin Hausawan Aba, Shehu Bello ya shaida wa wakilinmu cewa, gwamnan ya fara da yin tir da harin da aka kai kafin ya tabo batun biyan diyyar.
Ya ce, abin da gwamnatin ta biya bayan taron shi ne, diyyar dabbobin da aka kashe, kimanin shanu 56 daawaki 50. “A kan kowacce saniya, gwamnati za ta biya N150,000 kuma za ta biya N50,000 kan kowace akuya, kuma gwamnan ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan biyu na diyya ga kowane ran mutum daya da aka kashe.
Shugaban al’ummar Hausawan ya kuma tabo batun binne mutum takwas, inda ya ce, mutum daya ne ya rage a dakin ajiyar gawa a lokacin.
“Lallai mun binne dukkan mutanenmu, sai mutum daya da ya fito daga jihar Filato.” Ya kuma yi magana kan bacewar mutane biyu da har yau ba a san inda suka shiga ba.
“Tun bayan da lamarin ya auku, babu wanda ya iya yin barci cikin shugabannin al’umarmu saboda irin harin da aka kai da kokarin da muke yi na tabbatar da an yi masu adalci.
Har ila yau, din nan akwai mutane biyu da suka bace da ba mu san inda suke ba in ji shi.