Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Ronaldo, Kane, Benitez, Favre, Torres, Dumfries, Soumare, babu tabbas

Cristiano Ronaldo
Shugaban Barcelona Juan Laporta na sha’awar hada Cristiano Ronaldo da Lionel Messi su yi wasa a kungiyarsa a kakar wasa mai zuwa, kuma a shirye yake ya yi musayar dan wasansa biyu domin Juventus ta amince Ronaldo, dan wasan gaba, mai shekara 36, ya bar kungiyar. (AS – in Spanish)
Manchester City ta ce a shirye take ta mika dan wasan gaba kuma dan Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 24, da Raheem Sterling, da wasan gaba na Ingila mai shekara 26 domin ta cima burinta na daukan Harry Kane daga Tottenham. An dai sa wa Kane farashin fam miliyan 150. (Times – subscription rekuired)
Manchester United na kan bakanta ta raba Pau Torres, dan wasan baya kuma dan kasar Spaniya mai shekara 24 da Villareal. (Manchester Evening News)
Rafael Benitez na dab da zama sabon kocin Everton bayan ya sake tattaunawa da masu kungiyar a karshen makon jiya, duk da cewa magoya bayan kungiyar sun nuna rashin amincewarsu. (Mirror)
Crystal Palace kuwa tattaunawa ta yi da Lucien Favre domin y maye gurbin Roy Hodgson amma da alama Everton ma na son daukan shi. (Guardian)
Atalanta na fuskantar matsaloli wajen tsawaita kwantiragin Matteo Pessina, dan wasan tsakiya dan kasar Italiya, bayan da kungiyoyi biyu – AC Milan da Roma su ka bayyana cewa su na bukatar dan wasan mai shekara 24. (Calciomercato – in Italian)