Katin zabe, dama ga jama’a su zabi shugabanni -Injiniya Magaji

Injiniya Dokta Magaji Muhammad Sani

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban kungiyar masu fasahar gyaran ababen hawa nakasada aka fi sani da NATA, Injiniya Dokta Magaji Muhammad Sani ya yi kira ga al’umma musamman ‘ya’yan kungiyar su tabbatar sun yi rijistar samun katin zabe da akayi a kasar nan.

Shugaban na NATA na kasa ya bayyana haka ne a Kano inda ya yi nuni da cewa, yin katin zaben ga duk wani dan kasa abu ne mai muhimmanci musamman a tsarin da ake na dikuradiyya wanda shi ne zai bai wa mutum dama da ‘yancin zabar shugabanni da yake da yakinin za su kwatanta masa adalci.

Ya ce, mutane da suke cin alwashin cewa, ba za su sake yin zabe a kasar nan ba saboda ba su gamsu da yanda wadansu da aka zaba suka tafiyar da mulki ba su yi abin da ya kamata ba, sauya tunani domin damar su ce ta yan kasa su zabi wanda suka gamsu da shi su kauda wanda ba su gamsu da shi ba ta hanyar zabe wanda kuma zaben nan sai da kuri’a ake yi ba.

Ya ce, kungiyarsu tanada dimbin mambobi a Arewa domin haka ya zame masu tilas su ja hankalinsu dana sauran jama’a duk wanda ba shi da katin yaje ya yi. Katin zabe shi ne zai kare mutuncin al’ummar ka da bangaren da kake a kasar nan.

Daga karshe, Injiniya Dokta Magaji Muhammad Sani ya yi fatan Allah ya bai wa shugabannin Nijeriya karfin gwiwa na yin abinda ya kamata su yi adalci su kuma talakawa Allah ya ba su ikon yin biyayya garesu ya kuma bai wa kasar nan zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin da zai saukakawa al’umma halin kuncin rayuwa da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *