Katsina, kungiyar kiwon lafiyar iyali za su rarraba gidan-sauro -Fiye da miliyan 5

Kin mallakar makamin kare kai, kuskure –Masari

Governor Masari

Tura wannan Sakon

Daga Muawuya Bala Idris, Katsina

Gwamnatin jihar Katsina hadin gwiwa da wata kungiya Society For Family Health za su rarraba gidan sauro fiye miliyan 5 kyauta ga iyalai a jihar. Mataimakin shugaba, Mister John Ocholi ya fadawa jaridar Albishir cewa, za a rarraba gidan sauron a farkon satin watan Maris na wannan shekarar.

Ocholi ya ce, za a yi kwana 12 ana rarraba gidan sauron a mazabu 361. Ya ce, rabon gidan sauron ya zama dole domin maye gurbin gidan sauro da aka rarraba a cikin shekerar 2018.

Ocholi ya ce, kowanne gidan sauro yana lalacewa shekaru uku zuwa hudu, wanda ya kamata a sauya shi domin kare lafiyar iyalai.

Ya ce, tuni aka shirya bitar makamar aiki ga jami’an lafiya 209 da aka zabo daga kananan kuhumomi. Haka kuma an kafa kwamitoci a matakin jihar da kananan hukumomin domin wannan aikin.

Ocholi ya bayyana cewa, Masari Katsina, kungiyar kiwon lafiyar iyali za su rarraba gidan-sauro -Fiye da miliyan 5 Fadakarwa an shigo da sarakunan Katsina da Daura da kungiyoyin addini domin samun nasara.

Ya gargadi iyalai da kada su sayar da gidan sauron, domin yana da amfani a garesu.

Ocholi ya ce, gwamnati tare da hadin gwiwa da Society For Family health sun umarci jamian tsaro domin kama duk wanda ya sayar da gidan sauro.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su kai rahoton ga jami’an tsaro ga duk wanda ya sayar da gidan sauron

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *