Kauran Bauchi ya kaddamar da noman damina, takin zamani

Kauran Bauchi ya kaddamar da noman damina,

Kauran Bauchi

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Gwamnan jihar Bau­chi, Sanata Bala Muhammed (Kau­ran Bauchi) ya kaddamar da shirin noma da sayar da takin daminan bana, a garin Nabardo cikin karamar hu­kumar Toro.

Kaddamarwar ga dukkan manoman jihar Bauchi dama makwabtar jihr Bauchi baki daya, saboda sanin daraja da muhimmcin noma

Gwamnan ya ce, yana son jihar Bauchi ta kasance mai dogaro da kanta ta har­kan noma musamman shek­ara da muke ciki.

Ya kara da cewa, gwam­natin jihar Bauchi, tana da masaniyar yadda ake sayar da taki a kasuwa da tsada wanda hakan bai dace ba, hakan yasa za mu sayar da taki da rahusa, NPK za ta sayar da shi a kan Naira dubu 15, Yuriya kuma Naira dubu 20.

Gwamnan ya ce, gwam­nati za ta rinka ware kashi goma na kasafin kudi domin samar da kyakyawar yanayi a harkar noman jihar Bauchi.

Daga karshe ya yi kira da jan kunne ga al’umma da su gujewa almundahanar taki wajen sauya ingantattacen taki zuwa ga gurbatattace kuma su sayar ga al’umma da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *