Kauran Bauchi ya nada sarkin Jama’are

Tura wannan Sakon

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammed ya nada Alhaji Nuhu Ahmad Wabi a matsayin sabon Sarkin Jama’are wanda sakataran gwamnatin (SSG) na jihar Bauchi ke wakilta, Barista Ibrahim Muhammed Kashim.

A cikin jawabinsa, Barista, Kashim ya ce, yanke shawarar nada Alhaji Nuhu Ahmad Wabi ya cancanta tare da yin kira ga al’ummar Jama’are nagari da su mara wa sarkin baya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Kafin nadinsa a matsayin sabon sarkin Jama’are na goma, Alhaji Nuhu Ahmad Wabi shi ne Yariman Jama’are, (babban dan marigayi sarki) kuma sakatare na din-din-din a ma’aikatan gwamnatin Bauchi mai ritaya.

A nasa jawabin sabon sarki, Alhaji Nuhu Ahmad Wabi ya gode wa gwamna Bala Muhammed da mutanen masarautar Jama’are bisa goyon bayan da suka ba shi tare da yin alkawarin ci gaba da biyayya da girmama sarkinsu.

Shugaban karamar hukumar Jama’are, Alhaji Sama’ila Jarma, ya ce, al’ummar Jama’are sun ji dadin nadin sabon sarki, inda sun yaba wa gwamna Bala Muhammed bisa irin kokarin da ya yi wajen bai wa jama’a abin da suke so a garin Jama’aren Masarautar ma kanta ta yi murna da nadin Alhaji Nuhu Ahmad Wabi a matsayin sabon sarkin Jama’are.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *