Kawo karshen ta’addanci: Matawalle ya yi wa jama’a albishir

Gwamna Bello Matawalle
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Nan ba da dadewa ba jihar matasalar ta’addanci a Zamfara za ta zama tarihi domin gwamnati ta yi tanadin matakan da za ta dauka domin dakile yawan kasha-kashe da ke faruwa a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar na musamman da yammacin ranar litinin biyo bayan wani kisan mutane da ‘yan ta’adda suka yi a jihar kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Hakan ya auku ne a kauyukan karamar hukumar Bukkuyum da Anka, inda ‘yan ta’addan suka kashe mutane 58 tare da kai farmaki kauyuka hudu a jihar.
Gwamna Bello Mohammed ya bayyana cewa harin baya-bayan nan da aka kai a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka na jihar ya biyo bayan farmakin da sojoji suka kai a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da Birnin Magaji inda jami’an tsaro suka fatattaki fitaccen jagoran ‘yan ta’addan na watau Bello Turji, wanda ke ta’addanci kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a yankunan da ake fama da rikici.
Gwamnan ya kuma jajanta wa daukacin al’ummar Jihar Zamfara bisa kisan kiyashin da aka yi wa al’umma a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka. Gwamnan ya bukaci da a ci gaba da gudanar da aikin soji a fadin jihar domin fatattakar ‘yan ta’addan da suka addabi