Kazallaha a Sakkwato: APC ta nuna wa Shekarau yatsa

Jam iyyar APC da ke Sakkwato ta shawarci tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da ya gaggauta karkata akalarsa zuwa Kano in har yana da wata kwarewa ko bajinta a siyasa a maimakon sanya baki a siyasar jihar Sakkwato.

Malam Ibra­him Shekarau

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Jam iyyar APC da ke Sakkwato ta shawarci tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da ya gaggauta karkata akalarsa zuwa Kano in har yana da wata kwarewa ko bajinta a siyasa a maimakon sanya baki a siyasar jihar Sakkwato.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Isa Sadik Acida, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai a Sakkwato ranar Litinin da ta gabata.

Alhaji Sadik Acida ya ce, ya zama wajibi jam’iyyarsa ta mayar da martani a kan jawaban da wadansu ‘yan kazallaha suke yi na soki-burutsu.

Shugaban ya ce, wadannan ‘yan kazallahar siyasar sun hada da Malam Ibrahim Shekarau, wanda a yanzu Sanata ne a majalisar tarayya mai wakiltar Kano ta tsakiya da kuma ministan shari’a, Abubakar Malami. Ya ce, Malam Ibrahim Shekarau ya kirkiri tarwatsa jam’iyyar APC a Kano amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba a inda ya karkato akalarsa zuwa Sakkwato domin ya gwada.

A saboda haka aka tunatar da shi cewa, Sakkwatawa ba kanwar lasa ba ne ya kuma sani cewa, ba tare da shi aka kafa jam’iyyar APC ba kama ya yi ya koma can Otuoke wajen mai gidan sa a jihar Bayelsa watau tsohon shugaban kasa GoodLuck Ebele Jonathan .

Babu shakka Malam Ibrahim Shekarau ya kasance matsoraci da ke tattare da damuwa a dalilin shan kaye da ya gaza tafiyar da shugabanci a jiharsa.

Turakin Acida ya ce, manufofinsa na ya tarwatsa jam’iyyar APC a jihar Sakkwato hakarsa ba za ta cim ma ruwa ba. Acida ya tabbatar wa Shekarau cewa, Sakkwatawa na nan daram cikin APC tare da nuna goyon bayansu 100 bisa 100 ga jagoran tafiyar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Da ya juya kan ministan shari’a, Abubakar Malami, Alhaji Sadik Acida ya shawace shi da ya gaggauta sauka daga kan kujerarsa a dalilin yin katobara a gidan wani dan siyasa a inda yin hakan ya saba wa dokar kasa. Ya ce, a matsayinsa ministan shari’a bai dace da ya yi hukunci a kan shari’ar da ke gaban kotu ba.

A saboda haka, aikata haka ya saba wa doka a inda ya rataya Kur’ani cewa, zai bi dokar kasa tare da aikata gaskiya a tsakanin al’umma.

Turakin Acida ya ce, a dalilin yanke hukunci ba bisa ka’ida ba, suna kira ga ministan shari‘a da ya gaggauta sauka daga kan kujerarsa a dalilin yin katsalandan ga kotu ko kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sauke shi.

Daga karshe, shugaban jam‘iyyar, ya yi kira ga mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa da ya kori Abubakar Malami daga jamiyyar bisa dalilin taka rawarsa na kokarin rarraba kawunan ‘yan jam’iyyar a Sakkwato da Kano da Kebbi da Zamfara da kuma jihar Kwara da makamantansu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *