Kazamar riba, musabbaabin boye man-fetur – NNPC

Tura wannan Sakon

Kamfanin albakatun man fetur na Nijeriya (NNPC) ya musanta zargin da ake yi cewa, yana shirin kara farashin litar man-fetur a kasar.

Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari a hirarsa ta wayar tarho, ya bayyana cewa, ‘yan kasuwa ne suka jawo dogayen layuka a gidajen mai a wadansu sassan kasar bisa tunanin idan an kara kudin sai su ci riba mai tsoka. “Abin da ya sa ake ganin wadannan layukan shi ne ajiye kayan da mutane suka yi da suka daina sayar da man da wadansu gidajen man da suka sayi man suka daina sayarwa ko suka rage sayarwa”. in ji Kyari.

 A cewar shugaban kamfanin ba shi da kudirin kara farashin a wannan watan na Maris.

 Ya kuma ce gaskiya ne batun da ake cewa karin farashin gangar mai na da nasaba da fargabar da mutane suke na cewa za a iya karafarashin man.

 Ya bayyana cewa “Cikin halin da ake ciki yanzu, idan aka ce za a sayar da man kamar yadda kasuwa ta kama, lallai ya fi Naira 160 da ake sayarwa, amma kuma tallafi ne da gwamnati take yi a kan kudin man kuma wannan shekarar babu cikin kasafin kudin bana”.

Shugaban kamfanin man na Nijeriya ya ce suna ci gaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago da sauran kungiyoyi da gwamnoni domin kayyade farashin da ba zai bai wa talaka wahala ba.

A fadarsa, duk da janye tallafin man, gwamnati za ta kyale ‘yan kasuwa su sa farashi amma tare da sa idon hukuma saboda “shi ake yi a kowace kasa, duk duniya shi ake yi kuma tsarin da ake domin a tabbatar da cewa, ba a cutar da talaka ba”.

 Ya kara da cewa gwamnati tana amfani da kudaden tallafin man wajen gina tituna da makarantu da asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *