Kidayar gidajen Makiyaya: Gwamnatin Ganduje ta kawo masalaha ta fuskar tsaro -Kanawa

Kidayar gidajen Makiyaya

gidajen Makiyaya

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Manoma da makiyaya da ke jihar Kano sun bayyana cewa, gudanar da kidayar gidajen makiyaya zai taimaka wajen samar da masalaha ta fuskar tsaro da zaman lafiya a tsakanin su tare da jaddada cewa wannan tsari ya zo a daidai loka­cin da ake bukatar sa.

Wakilin mu wanda ya gudanar da tattaunawa daban-daban da ma­kiyaya da kuma manoma a jihar ya rawaito cewa kowane vangare ya yi marhabin da shirin kidayar gidajen makiyayan wadanda suke zaune a gurare daban-daban na fadin jihar ta Kano musamman ganin yadda al’amuran tsaro ke tafiya a wannan kasa.

Sannan dukkanin wadanda suka tattauna da ALBISHIR sun nuna cewa ko shakka babu gwam­na Dokta Abdullahi Umar Gan­duje shugaba ne mai kaifin tunani da basira musamman saboda vullo da wannan shirin na gudanar da kidayar gidajen makiyaya kamar yadda aka tsara.

Ardo Alhaji Geza, shugaban makiyaya na Dam din Kunnawa, ya bayyana cewa “ Babu shakka muna marhabin da wannan shiri na kidayar gidajenmu saboda a gaskiya hakan zai bai wa gwam­

goyon baya da hadin kai ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a wannan fanni, tare da yin godiya ga gwamnatin Ganduje saboda kokarin da take yi wajen kyautata zamantakewar makiyaya a jihar Kano.

Shi ma a nasa tsokacin, wani makiyayi malam Buba Amadu daga karamar hukumar Kiru ya yi na’am da yunkurin gudanar da ki­dayar gidajen makiyaya ta yadda gwamnati za ta san masu wadan­nan gidajen da kuma adadin maki­yaya dake jihar saboda tsara wasu manufofin gwamnati cikin sauki.

Ya kuma jaddada cewa, a shirye makiyaya suke domin samun nasarar wannan aikin.

Alhaji Haruna Abdullahi daga karamar hukumar Rogo, wanda bab­ban manomi ne, ya sanar da cewa shirin kidayar gidajen makiyaya a jihar Kano abu ne mai kyau da alheri domin a cewarsa, hakan zai sanya a tantance makiyaya dake zaune guri guda da kuma masu wucewa zuwa wasu sassa na kasar nan ko sauran kasashen dake nahiyar Afirka.

Haka kuma manomin ya bayya­na cewa yin kidayar zai kuma nuna makiyaya na zahiri wadanda kawai kiwon dabbobinsu suka sanya a gaba domin gwamnati ta rika sanya su cikin jadawalin shirye-shiryen su na yau da kullum domin tabbatar da cewa ana zaune lafiya.

Dukkanin wadanda suka yi bayanai sun nuna gamsuwarsu bisa yadda gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin gwamna Dokta Abdul­lahi Umar Ganduje take daukar ky­awawan matakai na kyautata tsaro da zamantakewar al’uma ba tare da nuna kasala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *