Kilu ta ja bau: Kisan gilla ya jawo soke lasisin makarantun kudi

Kwamishinan ilimi, Sunusi Sa’id Kiru
Daga Mahmud Gambo Sani
Gwamnatin Kano ta soke lasisin gudanar da makarantu masu zaman kansu a jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Sunusi Sa’id Kiru ne ya sanar da daukar matakin, a lokacin da ya gana da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce, za a sake duba takardun lasisin makarantun da aka soke tare da sabunta su bayan tantancewa.
Kwamishinan ya kara da cewa, an kafa kwamitin da ya kunshi ma’aikatar shari’a, da hukumar tsaron farin kaya ta DSS, da ta Cibil Defence da sauran jami’an tsaro da za su duba batun sabunta lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da dubun dubatar jama’a ke ci gaba da nuna bacin rai kan kisan da Abdulmalik Tanko, mai makarantar Noble Kids Academy, da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano ya yi wa yarinya ‘yar shekara 5 mai suna Hanifa Abubukar.
Yarinyar, daliba ce a makarantar wadda a nan ne malamin nata ya binne gawarta, bayan shafe kusan watanni biyu yana garkuwa da ita. Bayan shiga hannun ‘yan sanda ne Tanko ya bayyana cewa, ya kashe Hanifa ne da gubar bera da ya saya kan Naira 100.