Kin mallakar makamin kare kai, kuskure –Masari

Governor Masari
Daga Muawuya Bala Idris, Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce, kuskure ne ga Addinin mutane su ki mallakar makami domin kare kansu daga harin ‘yan ta’adda.
Masari wanda ya yi magana da manema labarai, ya ce dole mutane ko al’ummar gari su mallaki makamai domin kare muhalinsu. Ya ce, ya zama abin kunya mutane su boye domin gudun harin ‘yan ta’adda ba tare da fitowa su kare kansu ba.
Masari ya fada cewa, matsalar tsaro matsala ce ta kowa da kowa, ba a kyale gwamnati ta yi maganin matsalar ba. Ya jaddada cewa, jami’an tsaro sun yi kadan su kare rayukan al’umma, ya ce, ‘yan sanda dubu uku a jihar Katsina ba su iya kare mutane miliyan takwas.
A kan zaben kananan Hukumomi, Masari ya ce jihar ta shirya domin gudanar da zaben a watan Mayu na shekarar 2022. Ya ce, tuni an kafa kwamiti wanda zai yi aiki da masu ruwa-datsaki wajen gudanar da zaben. Gwamna Masari ya ce, an samu tsaiko wajen gudanar da zaben saboda da karar da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar ta na kalubalantar gwamnatinsa na rushe zaben kananan hukumomi a shekarar 2015.
Ya ce, a yanzu kotun koli ta yanke hukunci, kuma ta umarci gwamnatinsa ta biya hakkoki na albashi ga shugabannin rusassun kananan hukumomi da kansilolin su. Da yake magana a kan zaben 2023, Masari ya bayyana ra’ayinsa na mika mulki ga ‘yan Kudu na kasar nan.
Ya ce, ya goyi bayan mulki ya koma ga ‘yan Kudu domin dorewar dimukradiyya da zama kasa daya dunkulalliya. Masari ya ce, wannan ra’ayinsa ne ba ra’ayin sauran gwamnoni ba kuma bai saba wa dokar kasa ba.