Kirkire-kirkire: Dalibin GSS Kiru ya kera fanka

Kirkire-kirkire: Dalibin GSS Kiru ya kera fanka

Dalibin GSS Kiru ya kera fanka

Tura wannan Sakon

Daga Zainab Sani Shehu Kiru

Daya daga cikin daliban makarantar GSS KIRU yamma dan aji 4 ya nuna fasaharsa ta kera fanka mai amfani da hasken rana.

Yaron mai suna Ahmad Adamu haifafen garin Kiru dan sheharu 14 ya ce, ya yi tunanin kera fankar ne mai amfani hasken rana domin yana da sha’awar kere-keren fasahar zamani duk da cewar ba wai ya ko yi hakan ba ne.

Ahmad ya ce, ya yi ta nazarin hanyoyin da zai bi domin gani hada fankar, duk da cewa, ina zuwa makaranta kuma ina da wajen da muke gyaran kayan wutar lantarki ganin wadansu kayan sababbabi ne amma za ki ga sun kone saboda karfin hasken lantarki, shi ya sa ni ma na ce bari in gwada ta wa fasahar ganin na kera fanka da ma kwai mai amfani da haske rana.

Shi ma shugaban makarantar, Alhaji Mahmud Sulaiman, ya bayyana jin dadin sa bisa kokarin da Ahmad Adamu ya yi. Daga karshe, ya yi addu’a bisa fasihin yaro da ma sauranyara masu san yin irin kirkire-kiren kayan zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *