Komai nisan jifa… Juma’a shugaba Buhari zai gabatar da kasafin ban-kwana

Yau shugaba Buhari ke gabatar da kasafin ban-kwana

shugaba Buhari

Tura wannan Sakon

Daga Mahmoud Gambo Sani

A yau shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai gabatar da jawabi kan kasafin kudi na shekara ta 2023 ga hadin-gwiwar majalisun tarayya.

Kasafin wanda zai kasance na karshe irinsa da gwamnatin tarayya,a karkashin shugaba Buhari,za ta gabatar. Ana kyautata zaton cewa,za a kiyasta kasafin a kan farashin gangar danyen man fetur a kan dalar Amirka 70.

A yayin da za a rinka hako gangar mai miliyan daya da dubu dari shida da casa’in 1.69m) a duk rana kuma za a musayar Naira da dalar Amirka a kan Naira 435 da kobo 57,sai tashin fara farashi zai kai mizanin kashi 17 cikin 100 da digo 16,a yayin da habakar tattalin arziki za ta kai kashi 3 cikin 100 da digo 75 a shekarar da ta gabata kuwa an sami an sami karin kashi 3 cikin 100 da digo 55.

Har ila yau,an yi la’akari da rashin kwanciyar hankalin siyasa a duniya,musamman yakin Rasha da Ukrain da matsalar tsaro a cikin gida da tashin gwauron zabo a farashin shigo da kayayyaki daga ketare da kuma faduwar darajar musayar kudade da sauran matsaloli birjik.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *