Korafin ‘yan-kasuwar Sabon Garin Kano, rashin biyan haraji

Alhaji Uba Zubairu Yakasai

Alhaji Uba Zubairu Yakasai

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sanusi Kano

Sau da yawa akan sami korafe-korafen wasu daga cikin ’yan kasuwar Sabon Gari da ke jihar Kano, kasuwar da take kan gaba a cikin kasuwannin da ake ji da su a jihar da ma Arewacin Nijeriya wajen tumbatsar kasuwanci da kuma samar da kudin shiga ga gwamnati.

Korafin da akan yi ya hada da rashin magudanan ruwa a cikin kasuwar musamman yanzu da ake lokacin damina, idan a ka yi ruwa ba shi da hanyar da zai bi ya fice, saboda karancin hanyoyin da ruwan zai samu ya wuce.

Wannan ne dalilin da ya sa wadansu daga cikin ’yan kasuwar ke kokawa ga gwamnati kan a sama masu hanyoyin ruwa a cikin kasuwar, kasancewar idan a ka yi ruwan sama babu inda mutum zai bi ya wuce, har sai bayan an gama ruwan sama da wasu lokuta.

A wani bangaren kuma, da yawan masu sana’a a cikin kasuwar, suna ganin gwamnati jihar Kano ba ta yi masu ayyukan da ya kamata ba, musamman yadda suke bugun kirji da cewar suna biyan gwamnati haraji amma kuma abin yayi tsit! kan wannan aiki da suke ganin bai taka kara ya karya ba ya gagara.

A jin tabakin shugaban kasuwar ta Sabon Gari da Albishir ta yi, Alhaji Uba Zubairu Yakasai, wanda darakta a ofishin shugaban kasuwar, Alhaji Muhammad Bashir Abdul ya yi magana a madadin shugaban kasuwar, ya ce, akwai matsalolin da suke da su, domin kuwa gwamnati jiha ta yi yunkurin gyaran matsalar kusan sau biyu a wasu bangarori na kasuwar amma ’yan kasuwar suke ganin zai iya kawo tsaiko da tasgaro a harkar kasuwancinsu na yau da kullum.

Ya kara haske kan irin yadda ya kamata a ce ’yan kasuwar suna mayar da hankali wajen samar wa gwamnati kudin shiga ta wannan ofis sakamakon shi ne ofishin da gwamnati ta fitar domin kula da lamuran ’yan kasuwar ta kowace fuska.

Sanin kowa ne babu abin da yake kawo ma jihar Kano kudin shiga sama da hada-hadar kasuwanci,wannan ne ya sa nake kallon idan har gwamnati ta san akwai matsalolin da za su iya kawo koma baya ga harkokin ’yan kasuwa a Kano lallai ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo wa kasuwannin aikin da zai ba su damar samun kudin shiga.

A daidai lokacin da Albishir take kokarin gudanar da bincike kan wannan matsalar, muka ci karo da wasu mutane guda biyu da suke aiki da ofishin shugaban kasuwar da suka ce tsawon wata uku zuwa hudu ba su sami albashi ba, wanda aka ce kudin shigar da ake samu ne daga kasuwar ake biyan albashin ma’aikatan da su, amma kuma idan ’yan kasuwar ba su biya ba ba za a sami damar biyan su ba.

A ganina idan ’yan kasuwar za su ci gaba da bayar da goyon baya wajen biyan gwamnati haraji, zai iya kawo canji da irin gabatar masu aikace- aikacen ci gaba tare da bayar da goyon baya, lokacin da gwamnati take amfani da haraji wajen aikin ci gaba ga al’ummarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *