Korona: An yi wa Tambuwal allurar riga-kafi

Korona: An yi wa Tambuwal allurar riga-kafi
Musa Lemu Daga Sakkwato
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal tare da mataimakinsa aka yi wa allurar rigakafin korona da likitansa ya yi masa, a karkashin kulawar kwamishinan Lafiya na jihar Dokta Muhammad Ali Inname.
A cikin karshen makon da ya gabata ne gwamnan da mataimakinsa, Alhaji Muhammad Manir Dan Iya aka yi wa allurar, tare da yin kira ga al’ummar jihar da su amince da yin allurar ba tare da nuna tsoro ko fargaba ba.
Gwamna Tambuwal ya ce, yin allurar na da muhimmanci ta fuskar tabbatar da koshin lafiya da masu iya magana kance riga kafi yafi magani.
Tambuwal ya kuma kalubalanci wadansu al’umma da ke yada labaran kanzon kurege cewa, babu annobar korona musamman a sashen da ke fama da zafi wanda hakan ba gaskiya ba ne.
Daga karshe, gwamna Aminu Tambuwal ya sake kira ga jama a da su su ci gaba da bayar da goyon baya ga jami’an lafiya domin a cim ma nasarar kawar da ita annobar da ke neman yin katutu a kasar nan.