KORONA: Shugabannin asibtin Aminu Kano sun yi allurar riga-kafi.

Daga 17 ga Maris,2021 zuwa 22 ga Maris,2021,an.yi wa likitoci da ma’aikatan asibitin Malam Aminu Kano fiye da 200,allurar riga-kafin kamuwa da annobar Korona.
A wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun mataimakiyar Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta asibitin,Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi,ta bayyana cewa,tun da farko sai da shugabannin sassan asibtin suka rufa wa babban daraktan asibitin, Farfesa Abdul-Rahman Abba Sheshe,baya wajen yi masa tasa riga-kafin.
Jim kadan da kammala yi masa allurar,babban daraktan ya yi kira ga daukacin ma’aikata da likitocin asibitin da fito a yi masu rlga-kafin domin mutanen gari su gani su kwaikwaya.
Tun da farko, sai da babban daraktan ya jagoranci taron gaggawa da daukacin shugabanni sassan asibitin,inda ya hore su da su wayar da kan wadanda ke karkashinsu kan muhimmancin fitowa a yi riga-kafin.
Hajiya Nafisat Adamu ta bangaren kula da allurar riga-kafi,ita ta jagoranci aikace-aikacen,a yau.