Kotu ta tabbatar wa matawalle matsayin gwamna

Matawalle ya zama jagoran APC a Zamfara

Bello Matawalle jagoran APC a Zamfara

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Cikin makon da ya gabata, babbar kotun tarayya da ke Gusau ta yi watsi da karar da ke gabanta na kalubalantar gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara kan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da kwamitin riko na jam’iyyar APC mai kula da tsare-tsare na musamman (CECPC) ya fitar a ranar Talata ta bakin Sanata John James Akpanudoedehe ya ce, bisa hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin, kotun ta ce, babu wani tanadi a cikin kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka yi wa gyara) wanda ya bayyana cewa, gwamna zai rasa kujerar sa a duk lokacin da ya koma wata jam’iyyar da ba jam’iyyar da aka zabe shi ba.

Ya kara da cewa, “A madadin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa, gwamna Mai Mala Buni, jam’iyyar na yaba wa bangaren shari’a bisa sake kare kundin tsarin mulkin kasa da kuma tabbatar da Alhaji Bello Muhammad Matawalle a matsayin gwamnan jahar Zamfara.

Ya ce, “Gwamna Bello Muhammad Matawalle yana da ‘yancin yin taro da tarayya dangane da fita ko shiga jam’iyyar siyasa ta hanyar amfani da ’yancinsa na yin tarayya da sashe na 40 na kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka yi wa gyara), zai iya sauya sheka zuwa kowace jam’iyyar da ya ga dama, kuma ya ci gaba da rike kujerarsa ta gwamnan jihar Zamfara.

Ya kara da cewa, “Jam’iyyar APC na taya gwamna Bello Muhammad Matawalle murnar wannan tabbaci da babbar kotu ta yi, babu shakka ci gaban zai bai wa gwamnatin gwamna Matawalle damar ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da dama na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *