“Ku kare kima da mutuncinku” – Garki ya shawarci kungiyar Editocin Nijeriya

Daga Mahmud Gambo Sani
Janar Manajan gidan rediyon Freedom na Kano, Alhaji Adamu Ismail Garki ya shawarci mambobin kungiyar Editoci ta Nijeriya da su ci gaba da kare kimarsu da mutuncinsu.
Ya bayar da wannan shawarar ce yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar Editocin Nijeriya reshen jihar Kano da Jigawa wadanda suka kai masa ziyara a shirye-shiryen kungiyar na gudanar da taron mambobinta na kasa na wannan shekarar wanda za a gudanar a Kano a ranar 30 ga watan Mayu, 2021.
Janar Manajan wanda ya nuna damuwarsa a kan abin da ya bayyana a matsayin mara dadi yadda wasu gidajen rediyo ke aiki wajen bin hanyoyi marasa kyau wajen yada labaran karya da kazafi da kuma bakaken maganganu ba kakkautawa, inda ya yi kira ga kungiyar ta Editocin da cewa lokaci ya yi da za su tsunduma wajen rubuce-rubuce domin magance wannan matsalar.
“Lokaci yayi da zaku nuna kanku wajen daidaita da gyara aikin jarida, idan ba ku yi da kanku ba, ba wanda zai yi “, in ji shi.
Alhaji Garki ya kuma koka kan abin da ya kira laulayin da ke faruwa a halin yanzu da ya mamaye kafafen yada labarai inda a yanzu masu rahoto suka fi sha’awar abin da za su samu a wurin da za a ba su aikin maimakon sadaukar da kai ga aiki.
Ya yi alkawarin hadin kan gidan rediyon Freedom domin samun nasarar zaben da kungiyar za ta gudanar a Kano.
Tun da farko, shugaban Kungiyar na kasa reshen jihar Kano da Jigawa Dokta Sule Ya’u Sule, ya fada wa Janar Manajan gidan rediyon Freedom cewa mambobin Kungiyar sun zo gidan rediyon ne domin neman goyon baya da hadin kai domin samun nasarar zaben da Kungiyar za ta gudanar a Kano.