Kungiya ta karrama basarakiya kan inganta rayuwar mata

Daga Danjuma Labiru Bolari, Gombe
Kungiyar mata ma’aikatan kwalejin ilimi ta Nijeriya, National Association of Women in Collage of Education (WICE) ta karrama Dokta Amina Haruna Abdul (Wakiliyar Tula) kwararriyar Malama a kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya FCE Gombe kan inganta rayuwar mata.
Dokta Amina ta share fiye da shekaru 27 tana karantarwa gami da inganta rayuwar mata marasa gata wajen ganin rayuwar su ta inganta.
Dokta Amina ta taka rawa sosai wajen ciro wa ‘ya’yan marasa galihu kitse a wuta ta hanyar ganin sun sami ilimi, kuma sun koyi wata sana’a da za su dogara da ita ko da a gidajen aurensu, saboda halin kuncin rayuwa da aka shiga wanda bayan sun taimaki kansu za su taimaki mazajensu.
Kungiyar WICE ta duba irin gudumawar da Wakiliyar Tula ta bayar a bangarorin da dama sakamakon haka suka bata lambar yabo a taronsu na kasa da suka gudanar a kwalejin ilimi ta tarayya da ke garin Okene.
Da take zantawa da wakilinmu a Gombe kan karramawar da aka yi mata ta ce, ta ji dadi matuka, kuma ba ta da wata kalma da za ta iya gode wa shugabannin kungiyar bisa lambar yabon wanda ba ta yi tsammanin ta ba.
Dokta Amina ta ce, an ba ta lambar yabon ne kamar yadda yake a rubuce a kan shaidar bisa jajircewa, wajen ganin mata da yara da daidaikun al’umma sun sami ingantacciyar rayuwa.
A cewar ta, ta dade tana fadi tashi wajen ceto rayuwar al’umma, musamman a wannan zamani da komai ya tabarbare wajen ganin ta kare muradunsu ta fadakar da su, sannan ta ilimantar da su kana ta tallafa masu daidai gwargwado, inda a wani lokacin ma har da shigar da su wuraren koyon sana’ar da za ta rike su a rayuwa ba tare da sun dogara da abin hannun wani ba.
Dokta Amina Haruna ta yi amfani da wannan damar wajen kira ga shugabanin kungiyar WICE da su ci gaba da jajirce wa wajen ganin sun cim ma manufofin kungiyar, ba tare da sun bari siyasa ko son zuciya ya shiga ciki ya kawo masu nakasu a sha’anin tafiyar da al’amuran kungiyar ba.
Daga karshe, ta ce, a haka ne za a samu ingantacciyar rayuwa a tsakanin al’umma wajen sanin matsalolinsu, musamman wadanda suka shafi rashin tarbiya da ta’adanci da kuma yadda za a shawo kansu su ragu a tsakanin al’umma.