Kungiyar masu sayar da magunguna ta jinjina wa Kano -Saboda hadin kai

Daga Wakilinmu
Kungiyar masu sayar da qananan magunguna ta jihar Kano, suna samun cikakkiyar haxin kai da goyon baya daga gwamnatin jihar Kano, a qarqashin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje savanin shekarun baya da qungiyar ta samu kanta a ciki.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban qungiyar ta jihar Kano, Alhaji Muhammad Nura Abubakar, a lokacin da ya ke tsokaci a kan watanni kaxan da jagorancin qungiyar .
Malam Nura Muhammad Wudil ya qara da cewa, bayan wannan qungiyar tana samun haxin kai daga ma’aikatar lafiy ta jihar da kuma hukumar da gwamnatin jihar ta samar wajen tsabtace qananan asibitocin da ke faxin jihar .
Hukumomin da ke bayar da tallafi daga qasashen waje suna bai wa sun kan bai wa qungiyar haxin kai da goyon baya. Ya ce, za su ci gaba da faxakar da al’ummar jihar manufofin qungiyar da kuma aikace aikacenta a qananan hukumomin jihar 44, saboda duk inda ka je za ka samu yankungiyar na gudanar da sana’ar sayar da magunguna irin na Bature, wanda a shekarun baya waxansu qabilu ne suka mamaye harkar sayar da magani a jihar Kano.
Har ila yau akwai da dama daga cikin masu sana’ar sun karanci harkar lafiya a a makarantun da ke jihar, wannan ya sa aka kwamitoci daban-daban domin qara bunqasa harkar lafiya a jihar Kano da qasa baki xaya, babban burinsa, Malam Nura Muhammad ya ga a lokacin shugabancin shi qungiyar ta samu gagarumin ta fannoni da dama musamman tsaftace harkar saye da sayarwa na magunguna da kuma kawar jabun magunguna masu sanya maye ko kuma wanda wa’adin su yak are.
Sai ya nuna matukar farin cikin shi akan yadda yankungiyar ke bad a hadin kai da goyon baya wajen ciyar da kungiyar a gaba.Shugaban ya yi kira ga gwamnatin Kano, da ta taimaka wa qungiyar da abin haya da kuma ofis domin gudanar da harkokin kungiyar .
Daga qarshe, ya nuna farin cikin shi a kan goyon baya da yake samu daga hukumar NDLEA da kuma NAFDAC da sauran su.