Kura, Madobi,Garun Mallam: Mata iyaye sun yi na’am da takarar Kwankwaso -Zainab Madobi

Tura wannan Sakon


Daga Ibrahim Muhammad

Mata a kananan hukumomin Madobi Kura da Garun Malam da ke jihar Kano, sun karbi tafiyar dan takarar majalisar wakilai ta tarayya a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, a zaben 2023.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin hadima a gidan Musa Iliyasu Kwankwaso, Hajiya Zainab Hussaini Madobi, a lokacin da take zantawa da manema labarai bayan kammala wani taro da ta gabatar ga matan kananan hukumomin.

Hajiya Zainab Hussaini Madobi ta ce, Musa Iliyasu Kwankwaso uban gidanta ne a siyasa saboda haka ya sa ta tara matan yakin domin ta tallafa masu, mata su ne kashin bayan al’umma sannan su suke fitowa zabe saboda haka ta yi kira da cewa, ranar zabe su tabbatar sun zabi Musa Iliyasu Kwankwaso ya zama dan majalisar tarayya, sannan kuma zu zabi Gawuna da Garo su zama gwamnan jihar Kano sannan Tinubu ya zama shugaban kasa.

Shima da yake na shi jawabin, Mujahid Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce, sun dauki lokaci suna shirya taro na motsa jam’iyyar APC a jihar Kano, ko kwanakin baya sun shirya irinsa a garin Madobi wanda ya tayar da hankulan sauran jam’iyya .

Daga karshe, Mujahid ya yi kira ga matasan jihar Kano su zabi APC tun daga kasa har sama idan aka samu nasara gwamnatin jihar za ta ci gaba da tafiya da matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *