Kuskuren PDP, rashin samun shugabanci -Aminu Wali

Aminu Wali
Daga Shafi’u Yahaya Ambasada
Alhaji Aminu Bashir Wali ya ce, rashin neman shugabanci da ba su yi ba tun farkon kafa jam’iyyar PDP daga jihar Kano da kuma shiyyar Arewa shi ne babban kuskuren da suka aikata. Wali ya yi wannan bayanin ne ya fito ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke Kano, kwanannan.
Dattijon, wanda tsohon jakadan Nijeriya ne a kasar Amurka da kuma Kasar Sin kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998 ya kara da cewa, mafi yawancin wadanda suka kafa PDP watau G34 kamar irin su, Salomon Lar da Ales Ekwueme da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
Ya kara da cewa, a nan Kano, an kafa jam’iyyar ne a gidansa, inda ya ce, “babban kuskuran dana ce mun yi shi ne, ba mu nemi shugabanci ba, domin a nan Kano, marigayi Abubakar Rimi ya yi da ni in nemi takarar gwamnan Kano na ki, na ce, takarar da na yi har sau biyu a NPN a 1979 da 1983 ta isa, kuma duk muka dauko ’yan takarar shugaban kasa daga kudancin kasar nan”.
Wali ya kara da cewa, “tun bayan fitowar tsohon shugaban kasa, Cif Olushegun Obasanjo daga kurkuku, ya zo nan Kano domin in taimaka masa a takararsa a 1999, inda ya zama shugaban kasa har zuwa 2007, ban taimaka masa ba, domin na gaya masa ni ina tare da Ales Ekwueme, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari, tun a lokacin da muka yi jam’iyyar NPN da shi.
Ales Ekwueme na taimaka wa kuma shi na so ya zama shugaban kasa a PDP”. A karshe Ambasada Wali ya ce, duk mukaman da ya samu a gwamnatin PDP bai taba neman wani mukami ba, ba shi kawai ake yi, inda ya ce, hatta jakadan Nijeriya a kasar Sin, marigayi shugaban kasa, Alhaji Umaru Musa ’Yar’adu’a ne ya kira shi ya ce, ya zo ya yi masa alfarma ya zama jakadan Nijeriya a kasar Sin.
Ya kuma shawarci `yan Nijeriya da su zabi Alhaji Atiku Abubakar a zaben shekarar 2023, domin shi kadai ne ya ke da gogewar da zai iya tafi da Nijeriya daidai, inda ya kara da cewa, rashin samun shugaban da ya dace a zabe mai zuwa, zai iya sa Nijeriya cikin mawuyacin hali.