Kyautata wa Abba zato, kishin Kano -Dahiru Arrow Dakata

Dahiru Arrow Dakata.

Dahiru Arrow Dakata.

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana babban abin da ya kawo nasarar NNPP a jihar Kano shi ne sakamakon irin ayyukan alheri da Kwankwaso ya gabatar a lokacin mulkinsa a baya wanda wannan alherin ne yake bibiyarsa.

Hakan tasa har yanzu duk abin da ya dauko a jihar Kano al’ummar Kano suke karba wannan ya kawo nasara. Tsohon sakataren kudi na jam’iyyar PDP na jihar Kano, Alhaji Dahiru Arrow Dakata ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Duk dan jihar Kano mai kishi dole ya yi wa gwamnatin Abba kyakyawan za to sakamakon kowa ya san shi mutum ne tsayayye kuma natsastse, jajirtaccen ma’aikaci mai so da tausayin al’ummar Kano.

Ya tabbatar wa al’ummar jihar Kano dana kasa cewa, da izinin Allah za su amfana da gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf gaba daya domin idan aka ce maganar Kano ta kasa ce gaba daya. Ya ce, al’ummar jihar Kano za su amfani gwamnatin Kwankwasiyya domin kowa ya san gwamnati ce da ke duba kasa take kallon talaka take so ta raya shi, ta daukaka jin dadin rayuwarsa.

Dahiru Arrow Dakata ya yi nuni da cewa, al’ummar jihar Kano sun baiwa gwamnati mai shigowa hadin-kai ta zabar Abba za su kuma ba shi hadin-kai za su kuma taya shi da addu’oi a kan mulki da za a fara a gama lafiya kowa ya amfana a jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *