Lukaku ya bai wa Tuchel hakuri -Kan laifin da ya yi wa Chelsea

Lukaku ya bai wa Tuchel hakuri -Kan laifin da ya yi wa Chelsea

Lukaku Romelu

Tura wannan Sakon

Romelu Lukaku ya bayar da hakuri zai kuma buga wa Chelsea Carabao Cup ranar Laraba da Tottenham in ji Thomas Tuchel.

Chelsea za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan farko na daf da karshe a Carabao Cup da za su kece raini a Stamford Bridge. Lukaku bai yi wasan da Chelsea ta tashi 2-2 da Liberpool a gasar Premier League ba ranar Lahadi, bayan wata hira da aka yi da shi mako uku da suka wu ce.

‘’Mun tattauna a tsakaninmu ranar Litinin, kuma zai dawo buga mana tamaula’’ in ji Tuchel – ya bayar da hakuri ya koma atisaye ranar Talata.’’

A hirar da aka yi da shi cikin watan Disamba, wanda Chelsea ta saya mafi tsada a tarihi kan fam miliyan 97.5 ya ce ‘’bana jin dadin’’ rawar da nake takawa a karkashin jagorancin Tuchel, kuma zan so na sake koma wa Inter Milan.

Tun kan ranar Lahadi Tuchel ya sanar cewar ya ajiye dan wasan mai 28 ba zai buga karawa da Liberpool ba, domin kada ya ci karo da matsala a shirye-shiryen da yake yi.

 Lukaku ya ci kwallo bakwai a karawa 18 tun bayan da ya koma Chelsea daga Inter Milan a watan Agusta. Dan kwallon tawagar Belgium na fama da jinya da rashin lafiya tun bayan da ya koma Stamford Bridge da taka leda, hakan ne ya sa wani lokaci baya buga wasanni yadda yake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *