Ma’aikata, a kama sana’o’in hannu -Matawalle

Gwamman Jahar Zamfara Matawalle
Gwamnan Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Bello Muhammad Matawalle, ya yi kira ga ma’aikata a fadin jihar su naimi sana’a domin dogaro da kansu bayn sun yi ritaya.
Matawalle ya bayyana hakane a wani bangare na bikin ranar ma’aikata ta duniya.
Yace yanzu gwamnatinsa na fama da biyan bashin da suka gada daga gwamnatin da ta gabata, na biyan albashi da kuma tafiyar da gwamnati ba ki daya.
Jaridar Albishir cewa, gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya yi buda baki da mambobin kungiyoyin ‘yan kwadago 36 karkashin shugabancin NLC a Gusau babban birnin Jihar.
An tabbatar da sabon mafikarancin albashi a Najeriya a matsayin doka a 2019 karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.
Kuma dokar ta yi bayanin kara kudin ne daga naira 18,500 zuwa naira 30,000.
“Zamfara wacce na daya daga cikin jihohin da suke karbar mafi karancin kudade daga gwamnatin tarayya ko wanne wata, ana cire mata sama da naira biliyan 1.6 daga kudin a matsayin bashin da ta gada daga gwamnatin baya” in ji Matawalle. “A kowanne wata ana barin jihar da kudin da ba su wuce naira biliyan 1.8 kuma tana biyan naira biliyan 1.3 ga ma’aikatanta 28,000