Madaba’ar Triumph za ta taimaka wa tsofaffin ma’aikatan CTV/ARTV

Triumph za ta taimaka wa tsofaffin ma’aikatan CTV/ARTV

Triumph za ta taimaka wa tsofaffin ma’aikatan CTV/ARTV

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Shuagaban madaba’ar jaridun Triumph, Malam Lawal Sabo Ibrahim ya yaba da kokarin tsofaffin ma’aikatan gidan talabijin na Abubakar Rimi wanda aka fi sani da CTV bisa hangen nasa wajen kirkiro kungiyarsu da manufar hada kan tsofaffin ma’aikatan wuri guda da kuma taimakekeniya a tsakaninsu domin cim ma nasara.

Malam Lawal Sabo ya yi yabon ne a lokacin da ‘ya’yan kungiyar karkashin jagorancin Injiniya Usman Sa’id suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa. Manajan Daraktan ya bayyana cewa, “Alakata da ma’aikatan CTV ta samo asali ne a shekaru masu yawa, tun lokacin da Marigayi Malam Umar Sa’id Tudun Wada yana aiki a gidan talabijin.

Fuskokinku da nake gani a yanzu dukkanku sanannu ne a wuri na, ko da ba zan iya ambato sunayenku daya bayan daya ba” Daga nan sai ya yi alkawarin bai wa kungiyar hadin kan da ya kamata wajen ganin ta cim ma nasarar da ake bukata, inda ya kara bayar da tabbacin cewa, kofarsa a bude take Daga shafi na farko wajen karbar kyawawan gudummawarsu da kuma shawarwarinsu.

Da yake gabatar da ‘yan kungiyar ga Manajan Daraktan madaba’ar, Editan jaridar Triumph wanda shi ma ya kasance dan kungiyar, Malam Muhammad Hamisu Abdullahi ya bayyana cewa, ya koyi abubuwa da dama daga kwarewar tsofaffin ma’aikatan gidan telebijin na CTV a lokacin da yake aiki a wurin.

Tun da fari da yake jawabi, shugaban kungiyar, Injiniya Usman Sa’id ya bayyana cewa, an kirkiri kungiyar ne domin ta kusanto da ‘ya’yanta wuri guda, da kuma kudirin tallafa wa junansu. “Mun zo nan ne a matKungiyar masu gudanarda magunguna na Musulunci. Alhaji Nasir Muhammad Nasir Albariyya na jawabi a taron. Wannan yarinyya bata ta yi, a taimaka mana da cigiya. Sunanta Fatsima. A Naibawa ‘Yan Lemo gidansu yake.

Ga lambar mahifinta Abubakar Mustapha 08067213986. sayin ‘yan kungiyar tsofaffin ma’aikatan gidan telebijin na CTV/ARTV, duk da cewa, ba mu gudanar da zaben shugabanni ba, mun zo nan ne domin mu gabatar da kungiyar sannan mu shaida maka irin manufofi da kuma dalilin da ya sa aka kirkiri kungiyar” a cewar shugaban. Ya kuma bayyana wa Manajan Daraktan cewa, kungiyar ta sami sahalewa ta rijista da hukumar da take yi wa kamfanoni rijista ta CAC domin tabbatar da cewa, aikin kungiyar yana tafiya a cikin tsari.

Daga bisani ya gode wa Manajan Daraktan bisa kyakkyawan shugabancinsa abin misali da kuma ci gaban da yake samarwa a madaba’ar ta Triumph.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *