Madalla da samun wadataccen ruwan famfo a Jigawa -Sakara Hadeja

Daga Abdullahi Sani Doguwa a Kano
An bayyana samar da ruwan sha mai cike da tsabta a yankunan karkara da ke fadin kananan hukumomin jihar masu amfani da hasken rana (SOLAR SYSTEM) da gwamnatin jihar Jigawa take samar wa a karkashin jagorancin gwamna Alhaji Abubakar Muhammadu Badaru.
Samuwar hakan ba karamin abin alfahari ba ne, ta fuskar magancewa al’umar yankunan karkarar matsalar rashin ruwan sha da ta dade tana ciwa al’umar yankunan karkara a jihar ta Jigawa tuwo a kwarya.
Tshon dan takarar majalisar tarayya daga yankunan kananan hukumomin Auyo da Hadeja da Kafin Hausa a jihar, kuma mai bai wa gwamnan shawara ta masamman kan harkar samar da ruwan sha mai cike da tsabta a fadin jhar baki daya shi ne ya bayyana hakan yayin da yake fayyace irin hobbasar da ofishinsa yake ga manema labarai, a gidansa da ke Hadeja.
Ya ce, tabbas gwamnatin jihar tare da ofishin kwamashinan ruwa na jihar, suna iya wajen ganin sun wadata jihar da ruwa mai cike da tsabta a koda yaushe.
Hassan Sakara ya bukaci al’ummar jihar Jigawa, da su ci gaba da bayar da goyan baya da hadin kai wajen ganin sashin ya ci gaba da wadata al’ummar jihar da ruwan sha mai cike da tsafta.
A karshe Hassan Musa (SAKARA) ya taya al’ummar kasar nan da ma jihar Jigawa murnar shiga sabuwar shekarar 2023, tare da fatan Allah ya hada mu da alherin da ke cikinta da kuma fatan za a yi zabe lafiya.