Madalla da shugabancin Lalong -Miyyati Allah

Taro kan gyara kundin tsarin mulki: Lalong ya furta ra’ayinsa

Gwamna Lalong

Tura wannan Sakon

Daga Mohammed Ahmad

Shugaban kungiyar Miyyati Allah na karamar hukumar Bassa, Ya’u Idris ya yaba wa gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong bisa zaman lafiya da aka samu, musamman a karamar hukumar Bassa inda yake shugabanta.

Ya’u Idris ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cikar jihar Filato shekaru 47, a taron da aka yi a filin Rawpam Township Stadium a ‘yan kwanakin nan da suka gabata. Idris ya bayyana cewa, “Su yanzu a Bassa sun gano inda matsalar take, saboda a baya an sami kuskure na rashin zaman lafiya, sannan babu wani alkhairi sai talauci, babu ci gaba, sai wani ya zo daga wani guri ya sasantasu”.

“Daga abu ya faru a Bassa sai ka ga ya yadu zuwa wasu gurare”, inda ya kara da cewa, suna fahimtar da juna ribar zaman lafiya, suna kuma gaya wa matasa amfanin zaman lafiya, wanda yawanci rashin zaman lafiyar su yake shafa, inda suke nusar da su soyayyar juna kamar yadda suka zauna da iyayensu a baya.

Ya ce, a bara, gwamnati ta yi musu alkawura ciki har da ginin kasuwa da makaranta, saboda matsalar da ake fuskanta a tsakanin Fulani da Iregwe a makaranta ko kasuwa.

Taron ya sami halartar Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Gbon Gon Jos, Gyan Buba da Sarkin Wase da sauran sarakunan jihar da kuma tsohon gwamna, Fidelis Tafgun da kungiyoyin kabilu wadanda suka yi bayani ciki har da Miyyati Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *