Madalla da sulhulta Doguwa, Garo -Kwamred Abdullahi Aliyu

Garo da Doguwa
Alhussain daga Kano
Sulhunta mataimakin dantakaran gwamnan jihar Kano a zaben shekara ta 2023, Alhaji Murtala Sule Galadima Garo, da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, babbar nasara ce da za ta bai wa jam’iyyar APC nasara a zabe mai zuwa.
Bayanin haka ya fito daga bakin baban daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Gawuna TB, Kwamared Abdullahi Aliyu, a lokacin da yake nuna farin cikinsa a kan sulhun da aka yi.
Kwamared Abdullahi Aliyu, ya kara da cewa, sulhun zai kunyata ’yan adawar jihar da suke ganin Alhassan Ado Doguwa zai iya ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar NNPP, babu shakka murnar ’yan adawar ta kuma ciki.
Babban daraktan ya kuma shawarci manya da kananan ’yan jam’iyyar ta APC da su hada kansu tare da hakuri da juna, sannan su kara shiri sosai wajen ganin Gawuna da Murtala sun sami nasarar samun gwamnatin jihar Kano.
Ya jinjina wa dan takarar gwamnan na APC, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, bisa yadda yake da nagarta da kuma son taimaka wa al’ummar jihar, sannan idan ya sami nasara zai bayar da muhimmanci ta bangarori da dama, musamman a kan ilimi da lafiya da kuma samar da wuraren koyar da sana’o’in dogaro da kai da sauransu.