Madrid za ta dauko Rudiger daga Chelsea

Madrid za ta dauko Rudiger daga Chelsea

Tura wannan Sakon

Real Madrid ta yadda za ta dauki mai tsaron bayan Chelsea, Antonio Rudiger a karshen kakar nan, in ji Guillem Balague.

Ranar Lahadi kociya, Thomas Tuchel ya sanar cewar Rudiger bai amince da kunshin kwantiragin da Chelsea ta yi masa tayi ba. Rudiger, wanda a baya ya tattauna da Bayern Munich kan batun komawa can, kungiyar Stamford Bridge ta yi masa tayin fam 200,000 a kowanne mako, amma bai amince ba.

Ana sa ran dan wasan mai shekara 29 zai saka hannu kan kwantiragin kaka hudu a Real Madrid, bayan an auna koshin lafiyarsa a Landan.

BBC ta fahimci cewar kudin da dan kwallon ya bukata kafin ya rattaba hannu kan yarjejeniya da wanda za a bai wa wakilinsa ne ya yi wa Chelsea tsada.

Rudiger, wanda ya koma Stamford Bridge da taka leda kan fam miliyan 29 daga Roma a 2017 ya kusan yi wa Chelsea karawa 200 da cin kwallo 12.

Ya kuma lashe kofuna a kungiyar da suka hada da na Champions League da Europa League da Club World Cup da kuma FA Cup.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *