Mafi karancin albashi a Edo dubu 40

Tura wannan Sakon

Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki ya bi sahun takwaransa na jihar Kwara wajen rage kwanakin aikin gwamnti a fadin jihar daga wuni biyar zuwa uku a mako.

A wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ranar Talatar da ta gabata, ta ce, matakin wani banagare ne na rage wa ma’aikata radadi da matakin cire tallafin man fetur zai haifar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “a matsayinmu na gwamnati mai hangen nesa, mun fara duba batun karin albashin ma’aikatan jiharmu daga 30,000 zuwa 40,000 mafi ka ranci, wanda ya zarta na kowace jiha a kasarmu’’.

“Haka kuma muna son tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da biyan kudin, yayin da muke fatan kara albashin, idan jiharmu ta fara samun kasonta daga kudaden da gwamnatin tarayya ta tara daga kudin cire tallafin man’’.

Haka kuma gwamnatin jihar ta ce tana sane da irin wahalhalun da matakin cire tallafin man ya haifar wa al’ummar jihar sakamakon karin kudin mota da na abinci da ma’aikatan jihar ke fuskanta.

‘’A don haka ne gwamnatin jiha ke sanar da cewa, ta rage wa ma’aikatan jihar kwanakin aikin gwamnati daga wuni biyar zuwa uku, inda za su yi aikin wuni biyun daga gida daga yanzu har zuwa wani lokaci nan gaba’’.

Sanarwar ta gwamantin jihar fitar ta umarci shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ke fadin jihar da su gaggauta tsara wa ma’aikatansu kwanakin da ya kamata su je aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *