Mai’aikatan jihar Bauchi na fama da talauci –Rahoto

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad Suleiman

Binciken kwakwaf da na yi a matsayina na dan jarida Mai’aikatan jihar Bauchi na fama da talauci -Rahoto mai binciken ya nuna mana cewa, sakamakon rashin ingantacciyar rayuwa, al’umnar jihar Bauchi suna cikin tsaka-mai-yuwa, ganin cewa kashi 75 cikin 100 na al’ummar jihar da albashin gwamnati suka dogara.

Daya daga cikin ma’aikatan da muka yi hira da shi ya shaida mana cewa, albashi yanzu a jihar Bauchi ba ya samuwa a kan kari, sakamakon gwamnati ba ta iya biyan albashi a kan kari, sai wani watan ya shiga, wannan ya jawo karin tallauci a tsakanin ma’aikata da jama’ar gari, ganin cewa, sai an biya albashi kasuwa take motsaya.

Da muka sami tattaunawa da wasu kananan ma’aikata a bakin sakatariyyar Bauchi, suna kokarin cin garau-garau, sun nuna vacin ransu ganin cewa duk mutumin da ya dogara da albashi a halin yanzu sai talauci ya kashe shi.

Babban abin bakin ciki shi ne, yadda gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad (Kauran Bauchi) ya fice daga jihar ya tafi neman takarar shugaban kasa ba tare da ya yi tunanin cewa, ma’aikatan Bauchi na cikin wani hali na talauci .

Duk kokarin da muka yi na jin ta bakin gwamnati ya ci tura, domin mai bai wa gwamnan jihar Bauchi shawara a vangaren kafafan yada labarai, Muktar Gidado, ya ki daukar wayar da muka yi masa, da kuma amsa sakon kar-takwana da na tura masa. Wata majiya ta kusa da shi ta ce, “Gwamnan ya hana duk wani kwamishina ko wani jami’in gwamnati magana da ‘yan jarida, ba tare da izininsa ba.

Kasuwanni Bauchi su ma wannan kamfar talauci ta shafe su, “domin kuwa, babu hada-hadar da aka saba kamar da, sai an biya ma’aikata albashi sanan harkokinsu suke motsawa.

A cewar wani mai awon kayan abinci, duk mai yawo a cikin garin Bauchi zai bayar da shaida kan yadda al’amura suka tsaya cik! babu wata hada-hada da annuri a idanun jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *