Majalisar Dinkin Duniya ta yi alwashin agaza wa Borno -Kan ta’addacin Boko Haram

Tura wannan Sakon

Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri

A ranar Talatar da ta gabata, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Mista Antonio Guterres, ya ce a shirye yake domin bayar da goyon baya ga yunkurin da ake yi wajen kawo karshen ta’addacin masu tayar da kayar baya a Arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya ce, wannan wani mataki ne na samar da zaman lafiya a kasar da ta fi kowace yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Guterres ya kuma bayar da tabbcin ci gaba da bayar da tallafin jinkai ga jihar Borno, kamar sake gina muhallan mutanen da suka baro gidajensu zuwa gudun hijira da ke sansanonin ‘yan gudun hijira suna kuma son komawa gidajensu cikin aminci da mutunci.

Sakataren majalisar dinkin duniya, ya ziyarci wani sansanin da wadansu mayakan da suka mika wuya da kuma ‘yan gudun hijira da ke sansanin Gubio a birnin Maiduguri.

Daga baya ya shaida wa taron mane ma labarai cewa, shirin mayar da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu zai taimaka wajen samun zaman lafiya.

Da yake jawabi, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce, akalla mayakan Boko Haram dubu 40 da iyalansu suka mika kansu ga hukumomi tun a shekarar da ta gabata, a daidai lokacin da kungiyar ke fama da mutuwar shugabanta a farkon shekarar 2021, kuma kungiyar ISWAP ke neman kwace su. Gwamnan ya ce, yana bukatar samar da sababbin wurare domin samun damar sake hadewa da tsofaffin ‘yan ta’adda da tsoffafin mayakan tare da alkawarin za su bayar da goyon bayan aikin.

Sakataren majalisar dinkin duniyar, kafin ya bar Borno sai da ya gana da wadansu daga cikin mayakan Boko Haram da suka tuba suka mika wuya da ke sansani da aka kebe su domin canza masu tunani kafin hada su da jama’arsu.

Nijeriya dai ta shafe shekaru 13 tana fafatawa da ‘yan Boko Haram da ke da alaka da ISWAP a yammacin Afirka, inda rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyi barin gidajensu.

A wani bangare na kokarin kawo karshen ta’addanci, gwamnati na mayar da mayakan da suka mika wuya bisa radin kansu zuwa ga ‘yan uwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *