Majema ta yaye dalibai 228 karo na biyu

Tura wannan Sakon

A ranar alhamis din data gabata ne makarantar Majema ta yaye dalibai 228 a karo na biyu, makaranta ta fara ne tun daga firamare zuwa sakandare har zuwa matakin Diploma duk a karkashin darektan makarantar, Mista Ghali Musa Abba, daya daga cikin wadanda suka halartaci jarabawar karshen domin sanya ido shi ne, Dokta Sabo Sani.

Daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ya bayyana wa manema labarai cewa, kokari aiki ne na mutum daya na koya da koyar wa, a jihar Filato ya roki gwamnatin jiha da ta tarayya da su kawo masu dauki, saboda suna daukewa gwamnati wani aiki, koda ginin ajujuwa ne ko a kawo masu malamai.

Shi ma Darektan makarantar, Mista Ghali Musa Abba a tattaunawarsa da ‘yan jarida ya bayyanna cewa, ba su taba samun tallafin gwamnati ba, sai dai lokacin korona ne aka bai wa malamai goma albashin wata uku, kuma a lokacin akwai malamai guda 70 a makarantar haka aka rarraba, babu wani dan siyasa ko mai kudi da ya taba tallafa wa makarantar.

Saboda duk wanda ya kalli daliban zai san cewa, yara ne da suke da buri na zama wani abu a rayuwa, Darektan ya kara da cewa, sun dauko ABU ne daga Zariya suka kawo Jos kusa da su, saboda shaidar kammala makarantar zai zo da ABU ne ba Majema ba, ya kara da cewa, yawancin ci gaban da ake gani a wajen su suka kawo shi, shekaru uku zuwa hudu da suka wace.

Da suka fara karatu a wajen, da a iya Majema kawai ake yin firamare da sakandare, kafin a fara diploma a unguwar Ring road, sannan wannan ne karo na biyu da suka yaye dalibai a matakin diploma, inda bara aka yaye dalibai 63 yanzu kuma dalibai 228,domin dage da albashi ya ce suna kokarin biya amma a wannan karon, sun fuskanci matsala amma malaman suna tare da su.

Abin da ya ba su wahala shi ne, gini da suka yi yadda kayan gini suka yi tsada, amma ba sa wasa da albashin malamai, sannan daya daga cikin jigo a makaranta shi ne Malam Mujitaba Ali Baba,wanda shi ne rajistara a makarantar, ya bayyanna cewa,”sun sami ci gaba da dama, wannan shi ne karo na biyu da aka yaye dalibai kusan 300.

Wanda yawanci wadansu da aka yaye a baya yanzu haka sun sami admission sun ci gaba da karatu, ya yi kira ga wadanda aka yaye kar su tsaya su ci gaba, shi ma shugaban dalibai Zubairu, ya ce, yaye dalibai kusan 300, ba karamin aiki ba ne, ya kira gwamnati da ta tallafa wa makarantar, shi dai Ghali Musa Abba ana yaba masa da irin namijin kokarinsa a matsayinsa na matashi, kuma babu tallafin gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *