Makiyaya, Manoma sun yaba wa Ganduje -Kan Magance Rikici

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Manoma da makiyaya sun mika sakon godiya ta musamman ga gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, sabo­da daukar matakai da yake yi na dakile rikice-rikice tsakaninsu wanda hakan ta sanya ake zaune lafiya tsakanin wadan­nan muhimman vangarori guda biyu.

A wata ganawa da manoma da ma­kiyaya suka yi da wakilin Albishir, sun nunar da cewa, ko shakka babu, gwam­natin jihar Kano bisa jogorancin gwam­na Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana kokari matuka domin tabbatar da cewa, ana zaune lafiya tsakanin manoma da makiyaya ta hanyar ware guraren kiwo da inda dabbobi zasu rika wucewa ba tare da shiga gonakin manoma ba.

Sannan dukkanin vangarorin guda biyu sun hakikance cewa, rashin gura­ren kiwo da rashin fitar da hanyoyin da dabbobi za su wuce shi ne abin da ke kawo rikicin manoma da makiyaya wan­da wajibi ne a tashi tsaye wajen ganin an magance matsalar ta yadda kowane ban­gare za su ci gaba da sana’arsu watau noma da kiwo.

Da yake bayani ga wakilinmu, shug­aban makiyayan Dam din Kunnawa, Ardo Alhaji Geza ya ce,“ Gaskiya muna goyon bayan irin matakai da gwamnatin jihar Kano me dauka na kawo karshen rikice-rikice tsakanin mu da yan uwan mu manoma musamman ganin yadda gwamna yake vullo da sahihan hanyoyi na samar da guraren kiwo ga makiyaya da ware hanyoyin da dabbobin mu za su rika wucewa ba tare da sun ratsa gonakin manoma ba”.

Sannan ya jaddada cewa, suna zaune lafiya tsakanin su da manoman wannan yanki da Dam din Kunnawa shekara da shekaru, tareda rokon gwamna Ganduje da shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Ado Tambai Kwa da su hada hannu wajen sake datse wannan Dam wanda ya karye tun a farkon wannan damina amma har yanzu ba’a fara aikin gyaransa ba.

Shima a nasa tsokacin shugaban ru­kunin gonaki na “Musani Farms”, Alhaji Musa Sani yace ko shakka babu, gwam­natin Ganduje tana yin abin da ya kamata wajen magance yawaitar rigima tsakanin makiyaya da manoma musamman ganin yadda ake kokarin fitar masu da guraren kiwo da kuma hanyoyin da dabbobin nasu zasu rika wucewa batare da shiga gonakin mutane ba.

Sannan ya yi roko ga gwamnatin da a fadada samar da guraren kiwo da kuma hanyoyin da dabbobin za su rika bi su na tafiya kiwo a kowane sashe na fadin jihar ta Kano domin kawo karshen wadannan rikice-rikice da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya wanda ke jawo asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu yawa.

Wakilinmu wanda ya duba yadda manoma ke cinye filayen da aka ware do­min makiyaya da wadanda aka ware do­min dabbobi su rika bi suna wucewa, ya ruwaito cewa dole ne sai gwamnati ta tashi tsaye tareda kafa dokoki masu karfi mud­din ana bukatar ware guraren kiwo da na wucewar dabbobi domin kusan ko ina aka je za’a tarar cewa, wadannan gurare duk an sayar dasu ga manoma babu inda maki­yaya za su tsuguna sosai.

Sannan zai yi kyau a kafa wata doka wadda za ta haramta sayar da guraren kiwo da hanyoyin da dabbobi ke bi su tafi kiwo musamman yadda bincike ya nuna cewa, mahukumta wadanda suka hada wadansu daga cikin dagatai da masu uguwanni da hakimai da jami’ai na kananan hukumomi suna daga cikin rukunin shugabanni dake taimakawa wajen sayar da guraren kiwo domin su sami abin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *