Makomar ‘yan gudun hijira: Nijeriya, Nijar za su yi mukabala

Sabon shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya ce zai shiga tattaunawa da gwamnatin NIjeriya domin mayar da ‘yan gudun hijirar da suka tserewa matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriyar domin samun mafaka a kasar ta Nijar.
Matakin dai na daga cikin alkawuran da sabon shugaban kasar na Nijar ya dauka a lokacin da yake gabatar da jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi.
Yayin jawabin da ya gabatar, Bazoum ya koka kan yadda ta’addanci ya zamewa Jamhuriyar Nijar babban bala’i duk da cewa sansanonin ‘yan ta’adda, da ma shugabanninsu na wajen kasar.
Yayin ranstuwar kama aiki a ranar 2 ga watan Afrilu, sabon shugaban Nijar Ba zoum Muhammad da ya zargi mayakan dake kai hare-haren ta’addanci a sassan kasar da aikata laifukan yaki.
Nijar na fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi dake biyayya da kungiyar Al’kaida ko IS wadanda ke ketarawa cikin kasar ta bangaren yammaci daga Mali da Burkina Faso, sai kuma kungiyar Boko Haram da ke kaddamar da nata hare-haren bayan shiga kasar dta bangaren kudu maso gabashi daga Nijeriya.