Malam Abduljabar bai tuba ba -Gwamnati

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano, Dokta Tahar Adam, (Baba Impossible) ne ya bayyana haka.
A cewarsa sakon muryar Abduljabar ya fitar ba ta nuna cewa ya tuba ba, illa janyewar da yake cewa, ya yi, ya ce, duk wanda aka samu da laifin vatanci ga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam to babu maganar tuba illa zartar da hukunci a kansa.
Kwamishinan Harkokin Addinai na jihar Kano, ya ce, a yanzu haka suna kan rubuta rahoton da za su aikewa da gwamna Ganduje da shi domin daukar matakin da ya dace.
Daga karshe sai ya ja hankalin al’umma da su guji daukar doka a hannu, domin gwamnati ba za ta saurarawa duk wanda aka samu da yunkurin tayar da husuma ba.