Maleriya: Nijeriya ta amince da allurar riga-kafi

Allurar rigakafin malaria
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta amince a fara yi wa ‘yan kasar allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro mai suna R21.
Sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, an sanar da ministan lafiya da hukumar bunkasa lafiya a matakin farko game da wannan mataki na amincewa da riga-kafin don daukar matakan da suka dace na yin allurar ga jama’a NAFDAC ta kuma bukaci fadada gwajegwajen da ake yi ta yadda matakan za su kunshi nazarin illar da allurar ka iya yi a Najeriya.
Ta ce, za a yi amfani da riga-kafin ne wajen hana kamuwa da zazzabin maleriya ga kananan yara ‘yan wata biyar zuwa ‘yan shekara uku da haihuwa. Sanarwar ta NAFDAC ta ce ana samun zazzabin cizon sauro a duk fadin Najeriya, kuma kashi 97% na al’ummar kasar ne ke cikin hatsarin kamuwa damaleriya.
A cewar rahoton zazzabin cizon sauro na duniya na 2021, Najeriya ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar maleriya. Kashi 27% na masu kamuwa da zazzabin cizon sauro a duniya, ana samun su ne a Najeriya. Kuma kasar ce ta fi yawan mutanen da suka mutu sanadin zazzabin maleriya a 2020.
Haka zalika, Najeriya ce take da kiyasin kashi 55.2% na mutanen da suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro a Afirka ta Yamma cikin shekara ta 2020