Mallakar katin zabe: Jam’iyyar Matan Arewa ta yi wa mata nasiha

Hajiya Kubra Ibrahim Dankani

Hajiya Kubra Ibrahim Dankani

Tura wannan Sakon

Alhussain daga Kano

Jam’iyyar Matan Arewa ta jihar Kano, a karkashin shugabancin riko na Hajiya Kubra Ibrahim Dankani, ta yi kira ga matan jihar Kano da na kasa cewa, lallai lokaci ya yi da matan za su fito domin karbar katin zabe.

Hajiya Kubra ta kara da cewa, karin wa’adin karbar katin zaben da hukumar zabe ta yi hakika wata da ma ce da ya kamata al’ummar kasar nan su yi amfani da ita musamman ga wadanda ba su karbi katin ba.

Ta ce, katin zabe da shi ne mutum yake zaben shugaban da ya kwanta masa a rai, musamman wadanda za su kawo masu ci gaba a yankunnansu.

Dankani ta bayar da misali da cewa, mata su ne suka fi fitowa a ranakun zabe, inda ta karfafe su da su fito su yi katin zaben don ganin sun sami damar zaben shugaban da zai kare muradunsu.

Shugabar ta kuma yi kira ga shugabanni da su rika sanya mata a madafin iko na kasar nan, tun daga kan kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya, ganin yadda matan suke bayar da gagarimar gudummawa wajen ci gaban kasa.

Ta kara da cewa, mata suna da basira da kuma kwarewa a kan fannoni daban-daban, kuma su suka fi sanin matsalolin mata ‘yan’uwansu.

Malama Kubra Ibrahim ta kuma yi amfani da wannan damar wajen taya al’ummar Musulmin jihar Kano da na kasa baki daya murnar zagayowar idin babbar Sallah, sannan ta tunatar da wadanda Allah ya hore masu zuwa kasa mai tsarki domin yin aikin Hajji cewa, su sanya kasar nan a cikin addu’o’in da za su gudanar a lokacin aikin Hajjin, musamman addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Daga karshe, Hajiya Kubra Ibrahim Dankani, ta roki maza da su rika kyautata wa matayensu, ta ce abin kunya ne a ce ana samun wasu mazan suna cin mutuncin matayensu.

Ta kuma yi kira ga matan da su rinka yi wa mazajensu biyayya tare da yi masu addu’a musamman lokacin da za su fita wuraren sana’oinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *