Mambayya ta karbi bakuncin taron farfado da Arewa

Daga Aliyu Umar da Mahmud Sani
A ranar 14 ga Nuwamba, 2021 aka gudanar da babban taron neman hadin kai domin farfado da martabar Arewa da ke Nijeriya, a nahiyar Afirka ta yamma. Taron wanda ya gudana a dakin taro na gidan Mambayya da ke unguwar Gwammaja, cikin birnin Kano, ya sami halartar jiga-jigan ‘yan siyasa, ‘yan takarda, da ‘yan kasuwa da kuma dimbin jama’a masu kishin Arewa.
Da yake gabatar da jawabinsa, a matsayin babban bako mai jawabi, Farfesa Abdullahi Uba Adamu, ya yi tsokaci kan hanyoyin da za a bi wajen dawo da martabar Arewacin Nijeriya, kamar fahimtar bambancebambancen da ke tsakanin Arewa na yawan jama’a masu amfani da yare fiye da 320.
Ya ce, taken Nijeriya na 1960 yana dauke da sinadarin kishin kasa, da kaunar jama’arta, a yayin da taken da aka sauya a shekara ta 1978, sai a hankali.
Ya karkasa Arewa gida uku yana cewa, (1) akwai Hausawa (2) akwai munaHausa (3) sai muna Kano, inda yake ganin idan aka fahimci haka, za a dauko hanyar hada kai da zamantare babu tsangwama a Arewa.
A nasa jawabin, Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ta hannun Fagacin Kano, Alhaji Bello Habib Dankadai, ya bai wa masu shirya taron tabbacin samun goyon baya daga masarautar Kano, kuma ya gayyaci shugabannin kungiyar zuwa domin tattaunawa, da musayar ra’ayi kan inda za a dosa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Alhaji Bashir Usman Tofa, ya furta cewa, zai yi jawabi da Hausa, bisa hujjar cewa, harshen Turanci shi ya jaza wa Nijeriya ta Arewa komabayan da ya dabaibaye ta.
Daga nan ya yi kira ga kungiyoyin hada kan Arewa da su duba yiwuwar narkewa, su zama kungiya daya, mai magana da yawun ‘yan Arewa, domin hankoron hada kan ya yi tasiri.
Shi kuma mai magana da yawun ‘yan kasuwa, Alhaji Bature Abdul’Aziz, ya ce, babu tarnaki game da hadin kai da ya wuce take-taken malamai da ‘yan siyasa, da ‘yan kasuwa da kuma shugabannin jama’a masu fada-a-ji.
Ya ce, muddin wadancan rukunan mutanen da ya ambata a baya, ba su daina rarraba kan jama’a ba, babu wata kungiya da za ta iya hada kan Arewa komai tasirinta.
Tun da farko, a cikin jawabinsa, shugaban kungiyar, Alhaji Gidado Mukhtar, ya fayyace fillafilla manufofi da sakon da kungiyar take dauke da shi ga jama’ar Arewacin Nijeriya, inda ya jawo hankalin al’umomin Arewa da su yi karatun ta-natsu, sun mara wa kungiyar, ta cim ma manufofinta na sake dawo da martabar Arewa.
Taron, wanda tsohon shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Ibrahim Umar ya jagoranta, ya sami halartar malamai, bisa jagorancin shugaban majalisar malamai, Sheikh Ibrahim Khalil, da ‘yan takarda, da manyan ‘yan kasuwa da kuma dimbin jama’ar gari, maza da mata.