Man-City ta ragargaza Man-United -A Premier

Tura wannan Sakon

Manchester City ta yi wa Manchester United shakar mutuwa, bayan doke ta -A Premier da ta yi da ci 4-1 a wasan mako na 28 na Premier.

KeBin de Bruyne ne ya fara zira kwallo ta farko a minti na 5 da fara wasan, wata shigar wuri da City ta yi wa United. Sai dai a minti na 22 ne kuma dan wasan United Jadon Sancho ya rama wa kungiyarsa bayan da Pogba ya taimaka masa wajen cin kwallon, abin da ya sa aka dawo kunnen doki a wasan kenan.

Mintina 5 da wannan farkiya, De bruyne ya kara zura kwallo ta biyu a rabar United bayan wani kokari da mai tsaron ragar kunigyar ya yi na hana cin kwallon da Barnardo SilBa ya buga masa, to sai dai kuma KeBin ya tabbatar da ita.

An juya hutun rabin lokaci United na da fatan rama kwallon da aka jefa mata guda, ita kuwa City da ke kan gaba na fatan ganin ta kara zuba kwallaye a raga.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokacin De Bruyne bai hakura ba sai da ya kara taimakawa Riyad Mahrez ya jefa tasa kwallon a minti na 68, abin da ya kara tabbatarwa da City nasararta.

A minti na 90 ne kuma Mahrez ya jefa kwallonsa ta biyu mai cike da rudani, wadda zai da aka duba na’urar da ke taimakawa alkalin wasa ta tabbatar da kwallon. Da wannan ne aka ta shi sakamakon wasa tsakanin Manchester (Birni da ta kauye ) kamar yadda magoya baya ke tsokanar juna da ci 4-1.

Wannan dai ya bai wa City damar kara zama daram kan teburin Premier da maki 69 wato maki 6 kenan tsakaninta da LiBerpool da ke matsayi na biyu, ko da yake tana da kwantan wasa guda. Wannan sakamako ya bai wa Arsenal da ke da kwantan wasa uku damar darewa matsayi na hudu a gasar, wato matsayin wadanda za su halarci gasar Champions a gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *