Man fetur: Gwamnati ta sanya batun janye tallafi a mala

Man fetur: Gwamnati ta sanya batun janye tallafi a mala

Gwamnati Janye batun tallafi

Tura wannan Sakon

Gwamnatin tarayya ta sanar da janye shirinta na cire tallafin man fetur. Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana hakan a lokacin da ta bayyana a gaban ‘yan majalisar dokokin kasa a ranar Litinin da ta gabata, inda ta ce, gwamnati ta sake nazari kan matakin da ta shirya dauka, bayan amincewa

da kasafin kudin shekarar 2022. Ministar ta ce, an yi kuskure wajen zabar lokacin zartar da matakin janye tallafin mai kwata-kwata, inda ta kara da cewa, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gwamnati ta yanke shawarar ba za ta aiwatar da matakin ba, la’akari da hasashen cewa ,‘yan Nijeriya na fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki, kuma cire tallafin zai kara dagula lamarin tare Daga shafi na farko Wannan yarinyya bata ta yi, a taimaka mana da cigiya. Sunanta Fatsima. A Naibawa ‘Yan Lemo gidansu yake. Ga lambar mahifinta Abubakar Mustapha 08067213986. da kara jefa jama’a cikin karin kunci. A baya dai gwamnati ta bayyana cewa, an yi tanadin biyan kudin tallafin man fetur ne daga Janairu zuwa Yuni kadai, abin da ke nufin daga watan Yuli za a cire tallafin baki daya. A karshen makon da ya gabata, kungiyar kwadagon ta TUC ta gindaya wa gwamnati sharuddan da ta ce dole ta kiyaye kafin aiwatar da shirinta na cire tallafin man fetur nan da ‘yan watanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *